Monday, October 21, 2024

MENE NE KIMIYYA?

Muna rayuwa a wani ƙarni na fasaha wato technology. Mu duba dama da hagunmu duk abin da idonmu ke iya gani za mu ga cewa fasaha ce ta samar mana da wannan abin da idonmu ke ganin. Idan aka ce fasaha kar ka je da nisa, ka fara da ƴan ƙananun misalai da ke kewaye da kai, misali: kamar keke ko babur, haka nan agogon hannu, tukunyar girki, fitilar ƙwai, dutsen guga, taraktar noma, na'ura mai ƙwaƙwalwa, jirgin sama, da dai sauransu..


Lissafi, likitanci, ayyukan gudanarwa, gine-gine, zane, ƙere-ƙere, injiniyanci, magana, kai har sarrafa abinci duk fasaha ce.

Samuwar fasaha ce ta sanya a yau mutum ke danganta kansa da sana'arsa. Fasaha ta sauƙaƙa abubuwa da dama da a da ake ganin rashin yiwuwarsu.


Ra'ayoyin mutane.

Wasu na ganin fasaha na nufin samar da abebaɗan da za a iya sarrafawa ne, wasu kuma na cewa tunanin sarrafa abin ko samar da shi shi ne fasaha. Sai dai, bayyana asalin mene ne fasaha abu ne mai sauƙin gaske.

Misali: idan muka ɗauka cewa fasaha na nufin samar da ababen da za a iya sarrafawa ne, da ƙasashen da ke sayen irin waɗannan abebaɗai su ma an saka su cikin jerin ƙasashen da suka cigaba a fannin fasaha. Amma abin bai kasance haka ba, domin ba mai lissafa ƙasashen da suka tara wayoyi ko jirage da motoci a jerin ƙasashe masu cigaba, sai don samarwa da sarrafi shi.

haka kuma wasu na da ra'ayin cewa: iya sarƙafa wani abu cikin wani da basirar warware sarƙaƙiya a kimiyyance ne gaskiyar ma'anar fasaha. Ba za mu ce gaskiya ba ne. Domin fasaha na iya kasancewa abu mai sauƙi kuma tana iya zama mai wahala, sai dai tana iya kasancewa aiki da ke buƙatar nazari a kimiyyance.


Da wannan kyakkyawar fahimta tamu za mu iya cewa, ashe fasaha ita ce amfani da buɗaɗɗan ilimi da basirar da Allah Ya ba mu, tare da gwanancewarmu don samar da wani abu ko sarrafa shi cikin salo wanda za mu iya sake maimaita shi ko sake canja mai salo zuwa wani abun daban.

Ku kalli dama da hagunku duk abin da kuka gani ku nazarce shi tare da tunanin yadda aka samar da abin, ku yi tunanin yadda za ku iya sarrafa shi, ko ƙirƙirar taku. 

Fasahar Zamani


Tuesday, October 15, 2024

KASHIN KAJI


Duk yadda ka ga Babangida haka Buhari yake, sai dai shi Buhari kamar cinnaka yake 'bai san na gida ba': ma'ana yana da ɗabi'ar juya duk wanda ya yarda da shi.


31 Dec 1983, su Buhari da Babangida suka haɗu suka yi wa Shagari juyin mulki, amma Babangida sai ya bar wa Buhari mulki, ana nan sai Babangida ya samu labarin wainar da Buhari ke toyawa na shirin cafke shi, ai kuwa nan da nan Babangida ya ƙwace mulkin wannan ya faru a 27 Aug 1987.


Abin da Buhari bai sani ba game Babangida shi ne yana da yara a ko'ina cikin gidan soji, don haka duk shige da fice da ake yi suna sanar da shi. Wannan ne ya sa Babangida iya sake tsallake farmaki na yunƙurin juyin mulki da aka so yi masa a 22 Apr 1990.


Yau matsatsi da wai-ni-ƴasu da ake ciki Najeriya Buhari ne ya rubuta su kuma shi ne darakta, ya yi wa ƴan Najeriya halin nasa da ya saba, sai da ya tabbatar ya tsiyata Najeriya ta yadda wanda zai yi mulki bayansa abu biyu zai iya yi. 

Na farko shi ne ya sake ciyo bashi: wanda ba zai yiwu ba domin ƙasashen Turai sun riga da sun san halin da ƙasar take ciki.

Ko na biyu wanda shi ne a shaƙe wuyan talaka ta yadda za a iya samun wasu ƴan kuɗi daga wajensa kuma a cire shi daga nono wanda wannan tsarin Buhari ya ɗauka kuma ya ɗaura Tinubu inda daga ƙarshe ya bar sa da kashin kaji ana ta tsine masa.


Abin da ba ku sani ba shi ne zanga-zangar da kuke yi ba wanda zai saurare ku domin halin da kuke ciki da gangan aka saka ku, kuma an san dalilin yin zanga-zangar taku tin kan ku yi ta, sannan an san abin da za ku buƙaci a maku tin kan ku furta wanda abu ne da ba zai yiwu ba; dalili in har aka sakan maku wuya kuka wataya yadda kuke mafarkin yi to Najeriya ne za ta yi faɗuwar ƴan bori!


Ustaz 

15, Oct, 2024

Sunday, October 13, 2024

Fasahar Zamani.

 Howard Hathaway Aiken yana daga cikin waɗanda suka fara bunƙasa harkar lissafi, ta hanyar samar da na'urar lissafi da muke kira kwakwuleta. 

An haifi Aiken ranar 8 ga watan Maris ta shekarar alif da ɗari tara daidai (1900), a Hoboken, New Jersey. 

 Ya girma a Indianapolis, Indiana. A nan ya soma aiki kuma yana karatun engineering ɗinsa.

 Ya samu B.A a University of Wisconsin yana da shekara 23 a duniya. 

 Zuwa alif da ɗari tara da talatin da biyar (1935), Aiken ya shiga aiki kan ka'idojin gudanarwa na lantarki da ke buƙatar lissaffe-lissafe masu ɗankaren wahala.

 Da wannan ne ya shiga bincike na yiwuwar samar da wata fasaha da za ta iya taimakawa, sauƙaƙa lissafi cikin sauri da sauƙi. A lokacin yana ɗalibin doctorate digree (digiri na uku) a Harvard. Kuma a nan ne ya zaburar da da yawa kan wannan aiki nasa cikinsu akwai Thomas Watson.. 

A alif da ɗari tara da talatin da tara (1939) IBM ( International Business Machine) ta sa hannu kuma ta samar da nau'urar kwakwuleta ta farko.

Howard Aiken ya mutu 14 ga watan Maris ta alif da ɗari tara da saba'in da uku (1973) wato yana da shekara 73, a St. Louis, Missouri.  



Dissociative Identity Disorder (DID)

 Mutum ne ka san shi, ka saba da shi har halayyarsa ka naƙalta, kwatam sai ka ga ya sauya murya, halayyarsa ma sun sauya, kana masa magana z...