Friday, May 30, 2025

YADDA ZA KA BA WA SYSTEM ƊINKA UMARNI TA ƊAUKE TA HANYAR RUBUTU A CMD

Ta yiwu kana so ka taƙaita lokaci da kake ɗauka a computer, ko za ka ba wa yara su ɗan yi wasa ko kallo, kana iya amfani da wannan hanyar don gaya wa computer "Idan lokaci kaza ya yi ki ɗauke" da zarar lokacin ya cika za ta ɗauke da kanta. 


To ga dai hanyar:

Ka danna Windows key + R

Zai nuno maka search bar sai ka rubuta CMD sai ka danna Enter.

A cikin CMD sai ka rubuta: shutdown /s /f /t 0

Idan ka rubuta haka sannan ka danna Enter nan take system ɗinka za ta mutu. 

Idan kana so ka saita lokaci, misali minti ɗaya sai ka rubuta shutdown /s /f /t 60, idan hour ɗaya ne sai ka canja /t 60 zuwa /t 3600, hour ɗaya na yi za ta ɗauke kanta. 


Bonuses:

Bayan ka ba ta umarni sai ka canja ra'ayi ka koma CMD ka rubuta: shutdown /a ka danna Enter, shi ke nan ka kashe umarnin da ka ba ta na farko.


CMD (Command Prompt)

/S → (Shutdown)

/F → ( Force)

/T → ( Time)

Lambobin da ke zuwa bayan /t (Time) seconds ne, idan kana so ka ce wa system ɗinka ta ɗauke bayan minti ɗaya /t 60 za ka rubuta, sannan akwai tazara (gaph) tsakanin /t da seconds ɗin da kake so ka rubuta.

No comments:

Post a Comment

Dissociative Identity Disorder (DID)

 Mutum ne ka san shi, ka saba da shi har halayyarsa ka naƙalta, kwatam sai ka ga ya sauya murya, halayyarsa ma sun sauya, kana masa magana z...