Duk yadda ka ga Babangida haka Buhari yake, sai dai shi Buhari kamar cinnaka yake 'bai san na gida ba': ma'ana yana da ɗabi'ar juya duk wanda ya yarda da shi.
31 Dec 1983, su Buhari da Babangida suka haɗu suka yi wa Shagari juyin mulki, amma Babangida sai ya bar wa Buhari mulki, ana nan sai Babangida ya samu labarin wainar da Buhari ke toyawa na shirin cafke shi, ai kuwa nan da nan Babangida ya ƙwace mulkin wannan ya faru a 27 Aug 1987.
Abin da Buhari bai sani ba game Babangida shi ne yana da yara a ko'ina cikin gidan soji, don haka duk shige da fice da ake yi suna sanar da shi. Wannan ne ya sa Babangida iya sake tsallake farmaki na yunƙurin juyin mulki da aka so yi masa a 22 Apr 1990.
Yau matsatsi da wai-ni-ƴasu da ake ciki Najeriya Buhari ne ya rubuta su kuma shi ne darakta, ya yi wa ƴan Najeriya halin nasa da ya saba, sai da ya tabbatar ya tsiyata Najeriya ta yadda wanda zai yi mulki bayansa abu biyu zai iya yi.
Na farko shi ne ya sake ciyo bashi: wanda ba zai yiwu ba domin ƙasashen Turai sun riga da sun san halin da ƙasar take ciki.
Ko na biyu wanda shi ne a shaƙe wuyan talaka ta yadda za a iya samun wasu ƴan kuɗi daga wajensa kuma a cire shi daga nono wanda wannan tsarin Buhari ya ɗauka kuma ya ɗaura Tinubu inda daga ƙarshe ya bar sa da kashin kaji ana ta tsine masa.
Abin da ba ku sani ba shi ne zanga-zangar da kuke yi ba wanda zai saurare ku domin halin da kuke ciki da gangan aka saka ku, kuma an san dalilin yin zanga-zangar taku tin kan ku yi ta, sannan an san abin da za ku buƙaci a maku tin kan ku furta wanda abu ne da ba zai yiwu ba; dalili in har aka sakan maku wuya kuka wataya yadda kuke mafarkin yi to Najeriya ne za ta yi faɗuwar ƴan bori!
Ustaz
15, Oct, 2024
No comments:
Post a Comment