Howard Hathaway Aiken yana daga cikin waɗanda suka fara bunƙasa harkar lissafi, ta hanyar samar da na'urar lissafi da muke kira kwakwuleta.
An haifi Aiken ranar 8 ga watan Maris ta shekarar alif da ɗari tara daidai (1900), a Hoboken, New Jersey.
Ya girma a Indianapolis, Indiana. A nan ya soma aiki kuma yana karatun engineering ɗinsa.
Ya samu B.A a University of Wisconsin yana da shekara 23 a duniya.
Zuwa alif da ɗari tara da talatin da biyar (1935), Aiken ya shiga aiki kan ka'idojin gudanarwa na lantarki da ke buƙatar lissaffe-lissafe masu ɗankaren wahala.
Da wannan ne ya shiga bincike na yiwuwar samar da wata fasaha da za ta iya taimakawa, sauƙaƙa lissafi cikin sauri da sauƙi. A lokacin yana ɗalibin doctorate digree (digiri na uku) a Harvard. Kuma a nan ne ya zaburar da da yawa kan wannan aiki nasa cikinsu akwai Thomas Watson..
A alif da ɗari tara da talatin da tara (1939) IBM ( International Business Machine) ta sa hannu kuma ta samar da nau'urar kwakwuleta ta farko.
Howard Aiken ya mutu 14 ga watan Maris ta alif da ɗari tara da saba'in da uku (1973) wato yana da shekara 73, a St. Louis, Missouri.
Mu lura ba shi ba ne ya fara samar da kwakwuleta, amma yana daga cikin waɗanda suka haɓaka ko inganta fasahar.
ReplyDelete