Old Major, shi ne wanda ya kunna wuta cewa lallai dabbobi sai sun sami yancinsu, ta hanyar yin juyin-juya-hali(Rebellion). Kuma sun cim ma hakan ta hanyar hada kai, wanda suka kira da "Animalism" . Wannan darasi ne
Wanda ya jagoranci tabbatar da ganin wannan independence shi ne Snowball, shugaba ne jajirtacce, himma, ilimi da basira; wanda a kullum yake bude kofa ga talakawansa domin su bayar da gudummawarsu a gwamnati domin a gudu tare a tsira tare. A don haka akwai commandment guda 7 da suka kirkira wanda daga ciki akwai cewa "All Animals are Equal".
A iya jagorancin da Comrade Snowball ya yi, an sami cigaba da yalwatar arziki.
Kwatsam sai Napoleon ya yi masa juyin mulki, kuma daga nan gizo ya fara sakar!
Animal Farm littafi ne da ya fede biri har wutsiyarsa game da yadda siyasar duniya take. Rashin adalci, bi-ta-da-kulli, romon baka; ga kuma uwa-uba yadda yan siyasa ke amfani da bambancin halitta ko yare don cim ma kudirinsu.
Ji nake tamkar George Orwell, a littafin Animal Farm, halin da Najeriya ke ciki yake bayyanawa a kaikaice.
