Mutum ne ka san shi, ka saba da shi har halayyarsa ka naƙalta, kwatam sai ka ga ya sauya murya, halayyarsa ma sun sauya, kana masa magana zai iya cewa bai ma san ka ba. Amma fa gangar jikin abokinka ne, sai dai ba shi ba ne a ciki! To fa! Ta yaya hakan zai yiwu?
Ƙwarai hakan na faruwa, kuma ba aikin aljanu ba ne, lalura ce da ake kira da Dissociative Identity Disorder (DID). Lalura ce da ke haifar da sabbin halaye, ɗabi'u da yanayi ga wanda ke da ita.
Mai wannan lalura duk lokacin da ta tashi zai iya canza salonsa, ɗabi'arsa har yanayin maganarsa da kuma sunansa, kamar dai mai taɓin aljanu. Zai iya cewa sunansa Ali Nuhu bayan minti 5 ya ce maka a'a shi Adam A. Zango ne.
Allah ya sa ka taɓa kallon film ɗin da Algaita ta fassara da suna "Maisuburbuɗa”, to wancan shirin film ne amma a gaske akwai masu irin lalurar!
Akwai wani Ba'amurke Billy Milligan, an cafke shi a shekarun 1970s da zargin aikata laifuka ciki har da fashi da makami, da fyaɗe. Amma daga baya aka gano ba shi kaɗai ba ne a jikin nasa! Yana ɗauke da wasu mutane, wasu halaye, wasu tunani, wasu karin harshe da sunayensu har guda 24 ciki har da wata mai suna Adalana wacce ƴar maɗigo ce, kuma ita ce wacce ta aikata fyaɗen da ake zargin Milligan!
Case ne da ya shahara har aka yi fina-finai ta dalilinsa, ciki har da Netflix series mai suna Monsters Inside: The 24 faces of Billy Milligan, Apple TV+ Series The Crowded Room, da kuma documentaries da littafai, ciki akwai littafin Daniel Keyes, The Minds of Billy Milligan.
Wani abu game da masu lalurar (DID) ita ce:
A ba lallai ya san akwai B ba, haka B ba ta san da A ba.
Kowa da tunaninsa da abin da yake tunawa, kowa kuma da salonsa ko ɗabi'arsa.
To me ke jawo Dissociative Identity Disorder?
Faruwar wani abu a rayuwarka da ya kiɗima ka ko ya gigita ka, ko tsangwama da takura, ko damuwa musamman lokacin ƙuruciya kan iya haifar da wannan lalura.

