Al'adar Indiyawa ta ba wa dangin miji sadaki yayin aurenta mai dogon zango ce, sai dai ita al'adar an gurɓata ta a yanzu.
Stridhan a da kudi ne ko wani abu mai daraja kamar fili ko kadara da dangin amarya ke haɗa wa amarya domin tsaronta.
Kyauta ce da amarya ke samu daga ahalinta koda wani abu ya same ta na ujila ko saki ko ma mutuwar mijinta.
Saɓanin da can yanzu al'amarin ya juye ya dawo abu da ya zama dole daga dangin amarya, kuma miji ake ba wa stridhan, sai kuma abin da ya so za a ba shi.
Duk da dokar haramta tambaya, bayarwa ko karɓar sadaki ta 1961 har yau ana ci gaba da yin sa a al'adance, dokar ta kasance a takardu ne kaɗai domin ba a hukunta kowa.
Indiya na daga cikin ƙasashe da ke da manyan alƙaluma a mata masu kashe kansu a duniya, inda a 2021 NCRB ta fitar da alƙaluma cewa kimanin mata 23,178 ne suka halaka kansu, duk da hukumar ba ta fito kai-tsaye ta ce saboda sadaki ba ne, ta alaƙanta sababin hakan da matsalolin aure da sadaki.
Haka kuma Indiya ta ciri tuta a ɓangaren yawan ƴan mata masu zaman kansu, inda a nan ma aka ce alƙalumanta sun kai ko zarta miliyan 3.
Tuni dai akwai ƙungiyoyi da ke faɗa da wannan al'ada a faɗin Indiya amma mutane na ganin ƙin biyan sadaki tamkar nuna gazawa ce a tarihin ahalinsu kuma abin gorintawa.💑
No comments:
Post a Comment