"Lokaci kuɗi ne" cewar Hausawa, tabbas lokaci ya ma zarta kuɗi, sai dai rayuwa.
Daga cikin ababen da ake amfani da su a yau mafiya shahara wajen auna lokaci (wanda kowa ya sani) akwai agogo.
Sai dai ba kowa ba ne ya san inda aka bi ko yadda aka yi har aka samar da shi, yana ganin lambobi dai. Misali: daga 1 zuwa 12, (zaɓi ne) kuma ya iya karatu saboda haka yana iya faɗin abin da agogo ya gaya masa.
Masu binciken ƙwaƙwaf sun gano duniya na juyawa a shatinta (axis) sau 1 duk bayan awa 24, wanda wannan shi ne kwana guda a gare mu. Hakanan kuma, duniyarmu na kewaye ƙwallon rana sau 1 cikin kwanaki 365.25
A cikin awa 24 rana kan zo tsakar duniyarmu sau 1, wanda da wannan ne aka samu ma'aunin AM da PM.
Misali: Idan agogo ya nuna 9:30 na dare (PM), yana nufin rana ta wuce tsakar duniya da 9:30. Haka idan ta safiya ce (AM) yana nufin 9:30 ke nan gabanin rana ta zo tsaka.
Tambayar shi ne, yanzu da duniyarmu da kuma rana ba sa motsawa da yiwuwar a sa mu lokaci?
No comments:
Post a Comment