Thursday, February 6, 2025

DUWATSUN ƘARFE

'Tama', kuza' (a Turance kuma 'ore', plural 'ores') wasu duwatsu ne waɗanda ake samo ƙarfe, baƙin ƙarfe, jan ƙarfe, zinari, da lu'u-lu'u. 

 

 - A nau'o'in ƙarfe akwai waɗanda mayen ƙarfe ke iya kama su, akwai kuma waɗanda ba ya kama su. 

 - Sai dai, waɗanda mayen ƙarfe ke kamawa yau da kullum, iska da ruwa na sa wa su yi tsatsa. 

 - Waɗancan nau'in da ba sa kama mayen ƙarfe kuma ba sa yin tsatsa komi daɗewa, su ne irin su aluminum (holoƙo, sanholo), kwano, jan ƙarfe, tagulla, azurfa, zinari, da sauransu. 


 Kowanne irin ƙarfe yana da irin nasa aikin ko amfani, wani riƙe zafi ko sanyi yake, wani lantarki yake riƙewa, wani kuma ƙarfi gare shi da za a iya dukan wani abu da shi. 


  Najeriya muna da irin waɗannan nau'in duwatsu, kamar su: Enugu, Bauchi, Nasarawa, Kogi, Plateau, Kano, Kwara, Abia, Anambra, Cross-River, Ebonyi, Benue. 


 Mu sani nau'o'in ore kala-kala ne, kuma kowanne da abin da  ya ƙunsa.


No comments:

Post a Comment

Dissociative Identity Disorder (DID)

 Mutum ne ka san shi, ka saba da shi har halayyarsa ka naƙalta, kwatam sai ka ga ya sauya murya, halayyarsa ma sun sauya, kana masa magana z...